Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana shirin gwamnatin sa na sake fasalin Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) domin mayar da ita hukuma mai ƙwarewa wajen tafiyar da harkokin zirga-zirga da tabbatar da tsaron masu amfani da hanyoyi.
Sanarwar ta zo ne bayan da gwamnan ya jagoranci wani sintiri na tabbatar da bin dokokin zirga-zirga a mahadar Kofar Fanfo, inda ya shafe sama da awa guda yana sa ido kan yadda direbobi da sauran masu amfani da hanya ke bin umarnin fitilun zirga-zirga.
A cewar wata sanarwa da Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gidan Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, gwamnan ya samu rakiyar Sakataren Gwamnatin Jihar, kwamishinoni da sauran manyan jami’an gwamnati yayin sintirin.
Gwamna Yusuf ya umarci direbobin motoci masu zaman kansu, na haya, masu baburan ƙafa uku (Adaidaita Sahu) da kuma masu tafiya a ƙasa da su riƙa bin dokokin zirga-zirga tare da mutunta fitilun hanya, yana mai jaddada cewa hakan na da matuƙar muhimmanci wajen kare rayuka da dukiyoyi.
Ya ce gwamnatin sa za ta sake fasalin KAROTA tare da ƙarfafa hukumar domin ta gudanar da ayyukanta cikin ƙwarewa, ta inganta kula da zirga-zirga, ta tabbatar da aiwatar da dokokin hanya da kuma bunƙasa al’adar bin doka a faɗin jihar.
Gwamnan ya kuma sake jaddada aniyar gwamnatin sa na samar da ingantaccen tsarin sufuri mai tsari da aminci ga al’ummar Kano.
Haka kuma, ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda wasu masu amfani da hanya ke ci gaba da karya dokokin zirga-zirga tare da yin watsi da sabbin fitilun hanya da aka girka, yana mai cewa bai kamata a bar wannan gagarumin aikin da aka kashe kuɗaɗe masu yawa a kansa ya zama abin kallo kawai ba.
A ƙarshe, Gwamna Yusuf ya gargaɗi hukumomin da abin ya shafa da su ƙara sanya ido kan masu karya dokokin hanya tare da hukunta su bisa tanadin doka, domin tabbatar da ana amfani da kayan aikin zirga-zirga yadda ya kamata.