Jam’iyyar PDP ta kammala tura bayanan Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami zuwa shafin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a matsayin ɗan takararta na gwamnan Jihar Gombe domin zaɓen shekarar 2027.
Ƙungiyar Pantamiyya ta bayyana cewa an sanya sunan Pantami a shafin INEC ne bayan ya samu tikitin takarar gwamna ba tare da hamayya ba a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.
Ta ce an gudanar da dukkan matakan ne bisa ƙa’idoji tare da sa ido daga jami’an INEC.
Ƙungiyar ta bayyana wannan a matsayin wani muhimmin ci gaba a tafiyar dimokuraɗiyya a Jihar Gombe, tana mai nuna kwarin gwiwar cewa Pantami zai kawo sauye-sauye idan ya samu nasara a babban zaɓen 2027.
Ta kuma yabawa tsohon Ministan Sadarwa da Darakta Janar na NITDA bisa irin gudunmawar da ta ce ya bayar a fannonin fasahar zamani, ilimi, tattalin arziki da bunƙasa matasa, tare da bayyana shirinsa na ci gaban Gombe idan aka zaɓe shi.