Watanni biyar bayan mummunan harin da ’yan bindiga suka kai ƙauyukan Woro da Nuku a Jihar Kwara, iyalan waɗanda aka sace sun ce har yanzu suna rayuwa cikin damuwa da rashin sanin halin da ‘yan’uwansu ke ciki.
Sun bayyana cewa har yanzu babu wani tabbataccen labari game da waɗanda aka yi garkuwa da su.
Al’ummar yankin sun ce sun tara sama da Naira miliyan 150 domin biyan kuɗin fansa, amma masu garkuwa da mutanen sun ƙi karɓar kuɗin, suna masu cewa bai kai adadin da suke buƙata ba.
Hakan ya sa iyalan suka koma gida ba tare da samun nasarar ceto ‘yan’uwansu ba.
Rahotanni sun ce a harin da aka kai a watan Fabrairun 2026, an kashe mutane sama da 260, yayin da aka sace mutane 176, ciki har da mata da ƙananan yara.
Har ila yau, an ƙona gidaje da dama, lamarin da ya jefa yankin cikin babban tashin hankali.
Mazauna yankin sun gudanar da zanga-zangar lumana tare da yin kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatin Jihar Kwara da su ƙara ƙaimi wajen ceto waɗanda ke hannun ’yan bindiga.
Sun ce suna jin kamar a manta da su duk da tsawon lokacin da aka shafe ba tare da an kuɓutar da mutanensu ba.
Sai dai a Najeriya, biyan kuɗin fansa domin karɓo wanda aka yi garkuwa da shi ya saɓa wa doka.
Duk da haka, iyalan sun ce babu abin da suke nema face a ceto ‘yan’uwansu cikin koshin lafiya, tare da ɗaukar matakan da za su kawo ƙarshen irin waɗannan hare-hare a nan gaba.