Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiƘungiyar Take It Back ta shirya gudanar da zanga-zanga kan tsaro a...

Ƙungiyar Take It Back ta shirya gudanar da zanga-zanga kan tsaro a Najeriya

Ƙungiyar Take It Back Movement ta sanar da shirinta na gudanar da zanga-zanga a sassa daban-daban na Najeriya a ranar 5 ga Agusta, 2026, domin nuna adawa da abin da ta bayyana a matsayin matsalolin da ke ci gaba da addabar ƙasar.

A cewar ƙungiyar, zanga-zangar za ta mayar da hankali ne kan matsalar rashin tsaro, tsadar rayuwa da kuma abin da ta ce na tabarbarewar tsarin dimokuraɗiyya a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Rahotanni sun nuna cewa masu shirya zanga-zangar sun ce manufarsu ita ce isar da saƙon damuwar ‘yan ƙasa cikin lumana, tare da kira ga gwamnati da ta ɗauki matakan da za su magance matsalolin da al’umma ke fuskanta.

Sai dai har zuwa yanzu, gwamnatin tarayya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da wannan sabon shirin zanga-zangar ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments