Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeMutumin da ya fi kowa tsawo a kasar Ghana ya rasu

Mutumin da ya fi kowa tsawo a kasar Ghana ya rasu

Ya mutu bayan jinya sakamakon ciwukan da suka kama ƙafafunsa

Shahararren mutumin da ya fi kowa tsawo a Ghana, Sulemana Abdul Samed, wanda aka fi sani da Awuche, ya rasu yana da shekara 33.

BBC ta ruwaito cewa Awuche ya rasu ne a ranar Litinin a Asibitin Koyarwa na Tamale, bayan an kwantar da shi domin yi masa maganin ciwukan da suka kamu a ƙafafunsa.

Ya shafe wani lokaci yana karɓar magani a Tamale, mai nisan kusan kilomita 160 daga garinsu na Gambaga da ke arewacin Ghana.

Mutuwarsa ta jefa al’umma cikin alhini a Arewacin Ghana, inda mutane da dama suka san shi saboda tsayinsa na ban mamaki da kuma kyawawan halayensa.

Ɗan uwansa, Sulemana Abdul Kudus, ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai karamci da tausayi, yana mai cewa rasuwarsa ta girgiza al’umma.

Ya ce:

“Kowa ya san irin karamci da kirkin da yake da shi. Tun daga lokacin da ya rasu har yanzu mutane na ci gaba da zuwa gidansa domin sanin abin da ya faru.”

An gano Awuche na fama da cutar gigantism ne yana cikin shekaru 20 da haihuwa. Lokacin da BBC ta yi hira da shi a shekarar 2022, tsayinsa ya kai kafa 7 da inci 4 (santimita 223), sai dai rahotanni sun nuna cewa ya ci gaba da tsawo kafin rasuwarsa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments