Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da ƙarfafa shirye-shiryen yaƙi da yunwa da ƙarancin abinci mai gina jiki a faɗin Najeriya.
Ta bayyana hakan ne a Akure, babban birnin jihar Ondo, yayin rabon kayan abinci ga marasa galihu ƙarƙashin shirin Renewed Hope Initiative (RHI), inda Hajiya Nana Shettima ta wakilce ta.
Ta ce manufar shirin ita ce tallafa wa yara, mata, nakasassu da sauran masu buƙata domin inganta rayuwarsu.
A cewarta, shirin rarraba kayan abinci ya fara ne tun watan Maris na shekarar 2024, kuma ana samar da manyan motocin kayan abinci guda biyu a kowane wata domin rabawa jihohi daban-daban.
Oluremi Tinubu ta jaddada cewa, “Babu wani ɗan Najeriya da ya kamata ya kwana da yunwa,” tana mai cewa wannan na daga cikin manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na rage talauci da inganta walwalar al’umma.
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya yabawa shirin, yana mai cewa ya wuce rabon kayan abinci kawai, domin yana nuna tausayi da ƙudurin gwamnati na tallafa wa marasa galihu.
Ya kuma sake bayyana goyon bayansa ga Shugaba Tinubu tare da jaddada cewa jihar Ondo na mara masa baya a zaɓen 2027.