Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTsohon shugaban ƙaramar hukuma ya koma sana’ar ɗinki a Kano

Tsohon shugaban ƙaramar hukuma ya koma sana’ar ɗinki a Kano

Tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso ta Jihar Kano, Comrade Abdullahi Ghali Shitu, wanda aka fi sani da Basaf, ya koma gudanar da sana’arsa ta ɗinkin tela bayan kammala wa’adinsa na shugabanci.

Basaf, wanda ya riƙe muƙamin shugaban ƙaramar hukumar har zuwa watan Maris na shekarar 2026, ya bayyana cewa ya yanke shawarar komawa sana’ar da ya gada tun kafin shiga siyasa.

Ya ce sana’a na ba mutum kwanciyar hankali, ’yancin dogaro da kai da kuma tabbacin samun halal.

A wata hira da ya yi da Daily Trust, Basaf ya ce komawarsa sana’ar ɗinki ba wai saboda ya rasa abin yi ba ne, sai don isar da saƙo ga al’umma cewa bai kamata mutane su jingina rayuwarsu ga siyasa kaɗai ba.

Ya jaddada cewa sana’a ita ce ginshiƙin rayuwa da dogaro da kai, yana mai ƙarfafa musamman matasa da su mallaki wata sana’a ko ƙwarewa da za ta kasance abin dogaro a kowane lokaci.

Komawar tsohon shugaban ƙaramar hukumar sana’arsa ta asali ta ja hankalin jama’a, inda da dama ke yabawa matakin nasa a matsayin abin koyi da ke nuna mutuncin aiki da kuma darajar dogaro da kai.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments