Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiJigawa ta zama Jiha ta biyu mafi samun ci gaba a Najeriya...

Jigawa ta zama Jiha ta biyu mafi samun ci gaba a Najeriya – Rahoto

Jihar Jigawa ta zama jiha ta biyu mafi samun ci gaba a Najeriya, sannan ta zo ta farko a shiyyar Arewa maso Yamma, kamar yadda Rahoton Phillips Consulting State Performance Index (pSPI) 2026 ya bayyana.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Hamisu Muhammad Gumel, ya fitar, ya ce rahoton ya danganta wannan nasara da ingantaccen tsarin gudanar da gwamnati, kyakkyawan sarrafa kuɗaɗen jama’a da kuma nagartaccen aiwatar da manufofi da ayyukan gwamnati.

Rahoton ya tantance jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya bisa ma’auni 37 da suka shafi shugabanci da ci gaba.

An yi amfani da bayanan hukuma da aka tantance wajen bayar da kaso 70% na kimantawa, yayin da aka ware 30% ga ra’ayoyin al’umma.

Bugu da ƙari, rahoton ya nuna cewa Jigawa ta zo ta biyu a ƙasa wajen gamsuwar al’umma da ayyukan gwamnatin jihar, inda ta samu maki 3.69 cikin 5, abin da ke nuna karuwar amincewar jama’a da salon mulkin jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments