Wani babban jami’in kula da harkokin kuɗi na ƙungiyar ISWAP ya miƙa wuya ga dakarun Operation HADIN KAI, yayin da jimillar ‘yan ta’adda 46 tare da iyalansu suka ajiye makamansu a yankin Arewa maso Gabas.
Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa mutumin shi ne ke kula da harkokin kuɗi da samar da kayan aiki ga sansanin ISWAP da ke Jubillaram, inda ya miƙa wuya tare da ‘ya’yansa maza biyu.
A cewar rundunar, an ƙwato bindiga ƙirar AK-47, mujallu huɗu, harsasai 101, babur guda da kuma kuɗi har Naira 40,000 daga hannunsa.
Sojoji sun ce ci gaba da hare-haren ƙasa da na sama kan maboyar ‘yan ta’adda ne ya sa ake samun ƙarin masu miƙa wuya, lamarin da ke nuna cewa ƙarfin ƙungiyar ISWAP na ci gaba da raguwa.
Rundunar ta kuma buƙaci sauran ‘yan ta’addan da su ajiye makamansu, tare da kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin ƙarfafa yaƙi da ta’addanci.