Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasa2027: Tasirin mataimakan ’yan takarar shugaban kasa kan yaƙin neman zaɓe

2027: Tasirin mataimakan ’yan takarar shugaban kasa kan yaƙin neman zaɓe

Bayan manyan jam’iyyun siyasa sun bayyana ‘yan takarar mataimakan shugaban ƙasa, hankalin masu ruwa da tsaki ya koma kan irin rawar da za su taka wajen jawo ƙuri’u a babban zaɓen shekarar 2027.

Jam’iyyar APC ta ci gaba da tsayawa da Kashim Shettima a matsayin mataimakin ɗan takararta, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yayin da ADC ta zaɓi Rotimi Amaechi a matsayin mataimakin Atiku Abubakar.

A ɓangaren NDC, Peter Obi ya zaɓi tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin mataimakinsa domin ƙara faɗaɗa tasirin jam’iyyar musamman a Arewacin Najeriya.

Ana kuma ganin cewa Kwankwaso na da farin jini a tsakanin matasan Arewa da al’ummar Musulmi, abin da wasu masu sharhi ke ganin zai iya taimaka wa Peter Obi wajen ƙara samun karɓuwa a yankin gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Masanin siyasa, Suleiman Hassan Gimba, ya ce ba sunayen ‘yan takara kaɗai ne ke tabbatar da nasarar zaɓe ba, yana mai cewa tattalin arziki, tsaro, tsarin yaƙin neman zaɓe da yawan masu fitowa kaɗa ƙuri’a su ne manyan abubuwan da za su yanke hukunci.

A cewarsa, Kwankwaso na da ƙarfi wajen jan hankalin jama’a, Kashim Shettima na da gogewar shugabanci a Arewa maso Gabas, yayin da Rotimi Amaechi ke da ƙwarewa a fannin siyasa da mulki.

Shi ma malamin kimiyyar siyasa a Jami’ar Nnamdi Azikiwe, Dakta Christian Okeke, ya bayyana cewa Kwankwaso ne ke da mafi faɗin ƙungiyar magoya baya mai zaman kanta a cikin mataimakan ’yan takarar, sakamakon tasirin tafiyar Kwankwasiyya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments