Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaShugaban INEC ya yi alƙawarin zaɓe mai inganci da gaskiya a 2027

Shugaban INEC ya yi alƙawarin zaɓe mai inganci da gaskiya a 2027

Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa hukumar za ta gudanar da sahihin zaɓe a shekarar 2027, inda ya yi alƙawarin cewa za a ƙidaya kowace ƙuri’a yadda ta dace.

Amupitan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai wa tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), a gidansa da ke Minna, Jihar Neja.

Ya yabawa Abdulsalami kan gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa dimokuraɗiyya da tabbatar da zaman lafiya a Najeriya, musamman rawar da yake takawa ta hanyar Kwamitin Zaman Lafiya na Ƙasa.

Shugaban INEC ya ce duk da ƙalubalen da hukumar ke fuskanta, za ta tabbatar da cewa sakamakon zaɓen 2027 zai nuna ainihin zaɓin al’ummar Najeriya.

Hukumar ta kuma sanar da cewa za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya ranar 16 ga Janairun 2027, yayin da zaɓen gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi za su gudana ranar 6 ga Fabrairun 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments