Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiTinubu ya amince da daukar sabbin sojoji 28,000 domin karfafa tsaro

Tinubu ya amince da daukar sabbin sojoji 28,000 domin karfafa tsaro

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da faɗaɗa rundunar sojin ƙasa daga rundunoni takwas zuwa 12, tare da ba da izinin ɗaukar sabbin sojoji 28,000 domin ƙarfafa tsaron ƙasa da inganta ayyukan rundunar.

A cewar sanarwar mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, sabon tsarin zai ƙara inganta jagoranci, hanzarta kai ɗaukin sojoji wajen fuskantar barazanar tsaro, da kuma ƙarfafa kariyar muhimman ababen more rayuwa a faɗin ƙasar.

Matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin tarayya na bunƙasa ƙarfin rundunar soji da inganta yadda take tunkarar matsalolin tsaro da ke addabar sassa daban-daban na Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments