Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiAmurka ta kakaba harajin 12.5% kan kayayyakin da ake shigar mata daga...

Amurka ta kakaba harajin 12.5% kan kayayyakin da ake shigar mata daga Najeriya

Gwamnatin Amurka ta sanar da kakaba harajin kashi 12.5 cikin 100 kan wasu kayayyakin da ake shigar da su ƙasar daga Najeriya.

A cewar gwamnatin Amurka, matakin ya biyo bayan abin da ta bayyana a matsayin rashin aiwatar da ingantattun ƙa’idoji da dokokin samar da kayayyaki da suka dace da ƙa’idodin kasuwancin ƙasa da ƙasa.

Ana sa ran sabon harajin zai shafi masu fitar da kayayyaki daga Najeriya zuwa Amurka, tare da yiwuwar ƙara tsadar kayayyakin a kasuwar Amurka.

Har zuwa yanzu, gwamnatin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan sabon matakin da Amurka ta ɗauka ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments