Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiIyalan El-Rufai sun musanta wasikar da aka ce ya aika wa ADC

Iyalan El-Rufai sun musanta wasikar da aka ce ya aika wa ADC

Iyalan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, sun musanta wata wasika da ke yawo a kafafen sada zumunta wadda ake zargin ya aikewa shugabannin jam’iyyar ADC na ƙasa.

A cikin wata sanarwa da ɗansa, Mohammed Bello El-Rufai, ya fitar a madadin iyalan, ya bayyana cewa wasikar ba daga mahaifinsa ta fito ba, yana mai jaddada cewa rubutun hannu da abin da takardar ta ƙunsa ba su da alaƙa da shi.

Rahotanni sun nuna cewa wasikar da ake ta yaɗawa na ɗauke da zarge-zarge kan ɗan takarar gwamnan Kaduna na ADC, Isa Ashiru Kudan, dangane da batun rajistar jam’iyya.

Sai dai iyalan El-Rufai sun ce takardar ƙirƙira ce da aka yi domin haddasa ruɗani a cikin jam’iyyar.

Sun bayyana cewa wasu ne suka ƙirƙiri wasikar domin tayar da rikici da rarrabuwar kai a ADC, tare da neman bata sunan tsohon gwamnan Kaduna.

Iyalan sun yi kira ga jama’a da shugabannin jam’iyyar ADC da su yi watsi da takardar, suna mai cewa ba ta da inganci kuma wata ƙarya ce ta siyasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments