An gano gawar wani ɗalibi mai shekara 28 da ke karatu a Jami’ar Tarayya ta Kashere (FUK) a cikin wani ruwa mara gudana da ke ƙauyen Sabon Garin Yero, kusa da garin Kashere, a ƙaramar hukumar Akko ta jihar Gombe.
An bayyana marigayin da suna Enoch Sunday Maisamari, ɗalibi mai matakin karatu na shekara ta biyu a Sashen Microbiology na tsangayar Kimiyya ta jami’ar.
Bayanai sun nuna cewa Maisamari ya ɓace tun ranar Lahadi, bayan an gan shi a wani bikin kammala karatu da ɗaliban shekarar ƙarshe na jami’ar suka shirya.
Wata majiya ta ce ’yan sanda ne suka gano gawarsa a safiyar Talata, sannan suka tuntubi hukumomin jami’ar. Daga bisani, ɗaya daga cikin abokan karatunsa ya tabbatar da cewa gawar tasa ce.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ta samu rahoton gano gawar ne da misalin ƙarfe 9:30 na safiyar Laraba. Rundunar ta ce an kai gawar Asibitin Gwamnati da ke Kashere, inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce ba a ga wata alamar tashin hankali a jikin mamacin ba, amma ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano ainihin abin da ya haddasa mutuwarsa.