Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya yi ikirarin cewa Iran na neman a koma kan teburin sulhu yayin da take fuskantar matsin lamba, amma har yanzu ba ta nuna cikakken shirin cimma yarjejeniya ba.
Rubio ya bayyana hakan ne a wajen taron ƙasashen ASEAN da ake gudanarwa a Manila, inda ya ce gwamnatin Amurka za ta ci gaba da ƙara matsin lamba kan Iran muddin ba ta sauya matsayinta ba kan batun yarjejeniyar da ake tattaunawa.
A cewarsa, duk lokacin da aka yi ƙoƙarin cimma yarjejeniya da Iran, tana sauya sharudda ko kuma ta karya alƙawuran da aka cimma, yana mai cewa hakan ne ya sa Amurka ke ci gaba da tsaurara matakan matsin lamba.
Rubio ya kuma yi tsokaci kan mayakan Houthi na Yemen, inda ya zargi Iran da taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa ƙungiyar, yana mai cewa tasirin Tehran ya ƙara rura wutar rikicin yankin.
Sai dai har zuwa lokacin da Rubio ya yi waɗannan kalamai, Iran ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance da ke mayar da martani kan ikirarin nasa ba.