Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce idan jam’iyyarsu ta samu nasara a zaɓen 2027, za ta ɗauki sabon salo wajen magance matsalar rashin tsaro a Najeriya.
Kwankwaso ya bayyana cewa gwamnati za ta fara da dawo da amincewar jama’a ga hukumomin tsaro domin mutane su riƙa bayar da sahihan bayanai ba tare da tsoro ba.
Ya kuma ce za su buɗe ƙofar tattaunawa da masu aikata laifuka, ciki har da ‘yan ta’adda, domin nemo hanyoyin dakatar da tashin hankali.
Sai dai ya jaddada cewa wannan ba yana nufin za a daina amfani da ƙarfin soji ba, yana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da amfani da matakan tsaro masu ƙarfi tare da haɗa su da tattaunawa da haɗin kan al’umma domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro.