Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiBa za a kama Netanyahu a Amurka ba – Trump

Ba za a kama Netanyahu a Amurka ba – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ba za a kama Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, a Amurka ba, duk da takardar sammacin kama da Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ta fitar.

Trump ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, bayan kalaman Magajin Garin Birnin New York, Zohran Mamdani, wanda ya ce ofishinsa na nazarin yiwuwar kama Netanyahu idan ya ziyarci birnin.

Sai dai Trump bai yi ƙarin bayani kan yadda gwamnatin Amurka za ta aiwatar da wannan matsaya ba.

Lamarin na ci gaba da jawo muhawara a duniya, musamman dangane da takardar sammacin kama da ICC ta fitar kan Netanyahu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments