Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiLabaraiIran ta tsare jami’an diflomasiyyar Faransa biyu a Tehran

Iran ta tsare jami’an diflomasiyyar Faransa biyu a Tehran

Gwamnatin Faransa ta bayyana fushinta bayan zargin cewa jami’an tsaron Iran sun tsare jami’an diflomasiyyarta biyu a Tehran na tsawon sa’o’i tare da yi musu tambayoyi, inda aka kuma ce an ci zarafin ɗaya daga cikinsu ta hanyar duka.

Ministan Harkokin Wajen Faransa, Jean-Noël Barrot, ya ce lamarin ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa da ke kare jami’an diflomasiyya.

Ya tabbatar da cewa a saki jami’an kuma suna cikin ƙoshin lafiya, tare da shirin komawa Faransa.

Barrot ya kuma gargadi Iran cewa Faransa ba za ta yi shiru kan lamarin ba, yana mai jaddada cewa takunkuman Tarayyar Turai kan Iran za su ci gaba muddin ba ta dakatar da shirinta na nukiliya ba.

Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin da ke tsakanin Iran da ƙasashen Yamma ke ci gaba da ƙamari, yayin da Iran ke ci gaba da iƙirarin kai hare-hare kan wasu sansanonin sojin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments