Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ‘yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyun adawa, Atiku Abubakar da Peter Obi, ba su da isasshen ƙarfin siyasa a Arewacin Najeriya da zai ba su damar kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
Ganduje ya bayyana hakan ne yayin wani taro da aka gudanar a Kano, inda ya ce yankin Arewa na ci gaba da kasancewa muhimmin ginshiƙi a duk wani zaɓen shugaban ƙasa saboda yawan masu kaɗa ƙuri’a da tasirinsa a siyasar Najeriya.
A cewarsa, duk da tattaunawar haɗakar jam’iyyun adawa da ake yi, har yanzu bai ga wata alama da ke nuna cewa za su iya gina ƙarfin da zai ba su damar samun gagarumar nasara a jihohin Arewa ba.
Tsohon gwamnan Kano ya kuma buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sake nazarin ka’idojin rajistar jam’iyyun siyasa, yana mai cewa yawaitar jam’iyyu ba tare da ingantaccen tsari da akida ba na iya shafar ci gaban dimokuraɗiyya a ƙasar.