Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiBam ya kashe sojan Amurka a Iraq, adadin waɗanda suka mutu a...

Bam ya kashe sojan Amurka a Iraq, adadin waɗanda suka mutu a rikicin Iran ya kai 17

Rundunar Sojin Amurka ta CENTCOM ta tabbatar da mutuwar ɗaya daga cikin dakarunta a arewacin Iraq bayan wani bam ya tashi yayin da yake ƙoƙarin lalata bama-baman da ke jikin wani jirgin yaƙin Iran.

A cewar rundunar, lamarin ya faru ne a ranar 18 ga Yulin 2026, yayin da wani soja daban ya samu raunuka, amma an ce yana karɓar magani kuma ba a cikin mawuyacin hali yake ba.

Rahotanni sun nuna cewa mutuwar sojan ta ƙara yawan adadin dakarun Amurka da suka rasa rayukansu tun bayan barkewar rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran zuwa 17.

Haka kuma, an gano wasu sassan jikin mutum a ƙasar Jordan, inda ake ci gaba da bincike domin tantance ko na wani soja da ya ɓace ne.

A wani ci gaba, Firaministan Iraq, Ali Al-Zaidi, na shirin kai ziyara birnin Tehran domin tattaunawa da shugabannin Iran, bayan wata ganawa da ya yi da Shugaban Amurka, Donald Trump, a Washington.

Ana sa ran ziyarar za ta mayar da hankali kan dangantakar ƙasashen biyu da kuma batutuwan tsaro a yankin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments