Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiBago ya yi kira ga manoma da makiyaya su rungumi zaman lafiya...

Bago ya yi kira ga manoma da makiyaya su rungumi zaman lafiya a Neja

Gwamnan Jihar Neja, Umaru Mohammed Bago, ya yi kira ga manoma da makiyaya da su zauna lafiya tare da mutunta doka domin samar da zaman lafiya da ci gaban jihar.

Bago ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da limamai, shugabannin Fulani da wakilan manoma, inda aka tattauna hanyoyin kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya da ya daɗe yana addabar wasu sassan jihar.

Gwamnan ya yi gargaɗi ga limaman da ke amfani da mimbari wajen tunzura rikici tsakanin al’umma, yana mai cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wani wa’azi da zai haddasa fitina ba, kuma duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci.

Haka kuma, ya buƙaci shugabannin Fulani su ja kunnen matasan da ke haɗa kai da ’yan bindiga daga jihohin Sokoto da Zamfara wajen tayar da zaune tsaye, yana mai jaddada cewa duk wanda aka samu da hannu a aikata laifi zai fuskanci doka.

Bugu da ƙari, Gwamna Bago ya ce gwamnati za ta ɗauki mataki kan duk manomin da ya yi noma a wuraren da ba a amince da su ba, sannan ya haddasa rikici idan dabbobi suka shiga gonarsa.

Ya bukaci bangarorin biyu su rungumi zaman lafiya da bin doka domin ci gaban jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments