Ƙungiyar Tsoffin Sojojin Najeriya ta yi kira ga Babban Hafsan Tsaron Ƙasa da ya gaggauta tabbatar da aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin N250,000 ga jami’an sojojin Najeriya, wanda aka ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi tun a watan Nuwamban shekarar 2025.
Rahotanni sun nuna cewa tsoffin sojojin sun bayyana cewa lokaci ya yi da za a cika wannan alƙawari domin inganta walwala, rayuwa da kuma ƙara wa jami’an sojojin ƙwarin gwiwa wajen gudanar da aikinsu na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
A cewarsu, sojojin Najeriya na fuskantar manyan ƙalubale wajen yaƙi da ta’addanci, ’yan bindiga da sauran matsalolin tsaro, don haka ya dace gwamnati ta inganta albashi da sauran alawus-alawus domin su ci gaba da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Ƙungiyar ta kuma jaddada cewa aiwatar da sabon tsarin albashin zai taimaka wajen rage matsin tattalin arziki da ke addabar jami’an soji da iyalansu, tare da ƙarfafa gwiwar matasa masu sha’awar shiga aikin soja.
Sai dai, har zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga Ma’aikatar Tsaro ko Hedikwatar Tsaron Najeriya da ke tabbatar da cewa an fara aiwatar da mafi ƙarancin albashin N250,000 ga jami’an sojojin ƙasar.