Saturday, October 17, 2026
HomeKasuwanciAna fargabar tashin farashin fetur idan Dangote ya koma sayar da mai...

Ana fargabar tashin farashin fetur idan Dangote ya koma sayar da mai da Dala

Ana nuna fargabar cewa farashin fetur da dizal na iya ƙaruwa a Najeriya idan Matatar Dangote ta koma sayar da kayayyakinta da Dalar Amurka maimakon Naira.

Masana sun ce irin wannan mataki na iya ƙara buƙatar Dala a kasuwa tare da matsa lamba kan darajar Naira.

Rahotanni sun nuna cewa hauhawar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya, sakamakon rikice-rikicen da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, na daga cikin abubuwan da ke ƙara jefa kasuwar mai cikin rashin tabbas.

Idan aka fara biyan kuɗin mai da Dala, ana hasashen hakan zai iya ƙara farashin litar fetur da dizal a cikin gida.

A cewar wasu majiyoyi daga NNPCL, an samu ƙalubale a tsarin cinikin ɗanyen mai da ake yi tsakanin kamfanin da Matatar Dangote ta amfani da Naira.

An ƙirƙiro tsarin ne domin bai wa matatar damar sayen ɗanyen mai da kuɗin gida, tare da rage matsin lambar neman Dala da kuma taimakawa wajen daidaita farashin mai a Najeriya.

Sai dai, har zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga Matatar Dangote da ke tabbatar da cewa ta koma sayar da fetur da dizal da Dalar Amurka.

Don haka, rahotannin da ke yawo na nuna yiwuwar hakan ne kawai, ba tabbacin cewa an fara aiwatar da tsarin ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments