Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami, ya yi zargin cewa akwai wasu da ke ƙoƙarin shirya kai wa tawagarsa hari yayin da yake gudanar da rangadin siyasa a Jihar Gombe bayan sauya sheƙa zuwa jam’iyyar PDP.
Pantami ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Talata, 14 ga Yulin 2026.
Ya ce rangadin da ya kai ƙananan hukumomin Shongom, Kaltungo da Billiri domin ganawa da shugabannin jam’iyyar PDP ya samu gagarumar tarba daga magoya baya.
A cewarsa, bayan bidiyoyin tarbar da aka yi masa sun bazu, wani mutum da bai ambaci sunansa ba ya fara neman bayanan jadawalin tafiyarsa domin shirya abin da ya kira makirci a kansa da tawagarsa.
Pantami ya yi zargin cewa mutumin ya damu da irin karɓuwar da ya samu daga jama’a, lamarin da ya sa ya fara neman bayanan zirga-zirgarsa.
Sai dai bai gabatar da wata hujja a fili da ke tabbatar da zargin ba, kuma bai bayyana sunan wanda yake zargi ba.
Ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki da jami’an tsaro su tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma, yana mai tambayar yadda waɗanda suka rantse da kare jama’a za su bari a riƙa shirya makirci kan masu fafutukar siyasa.