Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiTsoffin sojoji sun nemi a fara biyan sojoji mafi ƙarancin albashin N250,000

Tsoffin sojoji sun nemi a fara biyan sojoji mafi ƙarancin albashin N250,000

Ƙungiyar Tsoffin Sojojin Najeriya ta yi kira ga Babban Hafsan Tsaron Ƙasa da ya gaggauta tabbatar da aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin N250,000 ga jami’an sojojin Najeriya, wanda aka ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi tun a watan Nuwamban shekarar 2025.

Rahotanni sun nuna cewa tsoffin sojojin sun bayyana cewa lokaci ya yi da za a cika wannan alƙawari domin inganta walwala, rayuwa da kuma ƙara wa jami’an sojojin ƙwarin gwiwa wajen gudanar da aikinsu na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

A cewarsu, sojojin Najeriya na fuskantar manyan ƙalubale wajen yaƙi da ta’addanci, ’yan bindiga da sauran matsalolin tsaro, don haka ya dace gwamnati ta inganta albashi da sauran alawus-alawus domin su ci gaba da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Ƙungiyar ta kuma jaddada cewa aiwatar da sabon tsarin albashin zai taimaka wajen rage matsin tattalin arziki da ke addabar jami’an soji da iyalansu, tare da ƙarfafa gwiwar matasa masu sha’awar shiga aikin soja.

Sai dai, har zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga Ma’aikatar Tsaro ko Hedikwatar Tsaron Najeriya da ke tabbatar da cewa an fara aiwatar da mafi ƙarancin albashin N250,000 ga jami’an sojojin ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments