Saturday, October 17, 2026
HomeIlimiGwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙarin kuɗin rajistar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙarin kuɗin rajistar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya ta sanar da dakatar da matakin da ta shirya na ƙara kuɗin rajistar jarabawar WAEC da NECO na shekarar 2027.

An ce an ɗauki wannan mataki ne domin ba da damar ci gaba da tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki kafin a yanke hukunci na ƙarshe.

Rahotanni sun nuna cewa Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta janye wasiƙar da ta fitar a ranar 18 ga Yunin 2026, wadda ta ƙunshi shirin ƙarin kuɗin rajistar jarabawar.

Hakan ya biyo bayan ra’ayoyi da korafe-korafen da jama’a da ƙungiyoyi suka bayyana.

A cewar gwamnatin, manufar dakatar da shirin ita ce bai wa masu ruwa da tsaki damar gabatar da shawarwari da kuma nemo mafita da za ta yi daidai da halin da ɗalibai da iyayensu ke ciki.

Matakin ya samu karɓuwa daga sassa daban-daban na al’umma, inda mutane da dama suka bayyana cewa dakatar da ƙarin kuɗin zai rage wa iyaye nauyin kashe kuɗaɗe, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar ƙalubalen tattalin arziki.

Ana sa ran gwamnatin za ta ci gaba da tattaunawa da hukumomin da abin ya shafa kafin ta sanar da matsaya ta ƙarshe kan batun kuɗin rajistar jarabawar WAEC da NECO ta shekarar 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments