Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da cewa zai sake tsayawa takara tare da Mataimakinsa, Murtala Sule Garo, a zaɓen gwamna na shekarar 2027.
Sanarwar ta tabbatar da cewa Garo ne zai ci gaba da kasancewa abokin takararsa yayin neman wa’adi na biyu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taro da ya yi da masu riƙe da muƙaman siyasa na gwamnatin jihar daga Kano, wanda aka gudanar a Gidan Gwamnatin Kano da ke Abuja.
A cewarsa, shawarar sake zaɓen Garo ta samo asali ne daga irin biyayya, ƙwazo da jajircewar da ya nuna wajen taimaka wa gwamnati wajen aiwatar da manufofinta tun bayan da suka hau mulki.
Abba Kabir Yusuf ya yaba da kyakkyawar alaƙar aiki da ke tsakaninsa da mataimakinsa, yana mai cewa Murtala Sule Garo ya nuna ƙwarewa, sadaukarwa da kuma iya gudanar da ayyukan da aka ɗora masa.
Gwamnan ya kuma yi kira ga shugabannin jam’iyya, masu riƙe da muƙaman gwamnati da magoya baya da su ci gaba da haɗa kai domin ƙarfafa nasarorin gwamnatin da kuma shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.