Hukumar Kula da Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar ambaliyar ruwa a jihohi 26 da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja tsakanin 11 zuwa 20 ga Yulin 2026, sakamakon ci gaba da samun ruwan sama mai ƙarfi a sassa daban-daban na ƙasar.
A cewar hukumar, jihohin Bauchi, Jigawa, Taraba, Adamawa, Plateau, Benue, Nasarawa da Kogi na daga cikin yankunan Arewa da ke cikin babban haɗarin
ambaliya.
Sauran jihohin da abin zai iya shafa sun haɗa da Kwara, Oyo, Ogun, Legas, Osun, Ekiti, Ondo, Delta, Edo, Abia, Imo, Ebonyi, Enugu, Akwa Ibom, Cross River, Rivers, Bayelsa da kuma Abuja.
NiMet ta bayyana cewa yawan ruwan saman da aka samu a farkon watan Yuli ya sa ƙasa ta cika da ruwa, lamarin da ke rage ƙarfin ƙasa na shanye ƙarin ruwa, wanda hakan ke ƙara haɗarin samun ambaliya musamman a wurare masu ƙasa da kuma yankunan da ba su da ingantattun magudanan ruwa.
Hukumar ta yi gargadin cewa ambaliyar na iya haifar da cikas ga zirga-zirga, lalata tituna da gadoji, katse wutar lantarki da hanyoyin sadarwa, tare da jefa harkokin sufurin jiragen sama cikin matsala saboda rashin gani yayin ruwan sama mai ƙarfi.
NiMet ta ce ambaliyar na iya lalata gonaki da amfanin gona, tare da ƙara haɗarin yaɗuwar cututtukan da ruwa ke haddasawa bayan ruwa ya ja baya.
Don haka, ta buƙaci mazauna yankunan da abin zai shafa su riƙa bibiyar hasashen yanayi tare da ɗaukar matakan kariya kafin da lokacin ruwan sama.