Wata Kotun Majistare da ke Jihar Katsina ta bayar da umarnin tsare malami a Ahmadu Bello University, Bashir Kurfi, bayan an gurfanar da shi kan zargin bata suna da kuma yaɗa bayanan da ake zargin ƙarya ne.
Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta gurfanar da Dr. Kurfi bisa tuhume-tuhume biyu ƙarƙashin sashe na 308 da 309(1) na dokar Penal Code ta jihar, sakamakon kalaman da ya yi a wata hira da Trust TV ranar 24 ga Yunin 2026.
A cewar rahoton farko da aka gabatar wa kotu, ana zargin Dr. Kurfi ya yi ikirarin cewa gwamnatin Jihar Katsina ta ɗauki nauyin aikin Hajji ga wasu da ake zargin shugabannin ‘yan bindiga ne.
Gwamnatin jihar ta musanta zargin, tana mai cewa ƙarya ce da ke bata sunanta tare da kawo cikas ga mutuncin al’ummar jihar.
Bayan an karanta masa tuhume-tuhumen, Dr. Kurfi ya musanta aikata laifukan da ake tuhumarsa da su.
Lauyan masu gabatar da ƙara ya roƙi kotun da ta ci gaba da tsare shi a hannun ’yan sanda har sai an kammala bincike, yana mai cewa bayar da beli a wannan mataki na iya shafar binciken.
Sai dai lauyan wanda ake tuhuma ya buƙaci kotun ta ba shi beli, yana mai jaddada cewa yana da haƙƙin kasancewa cikin ‘yanci yayin da ake ci gaba da shari’ar.
Bayan sauraren hujjojin ɓangarorin biyu, Alƙalin Kotun Majistare, Zaharaddeen Kofar Soro, ya ba da umarnin a ci gaba da bincike tare da tsare Dr. Kurfi a hannun ‘yan sanda har zuwa ranar 14 ga Yulin 2026, lokacin da aka ɗage ci gaba da sauraron shari’ar.
An mayar da Dr. Kurfi zuwa sashen binciken manyan laifuka (SCID) na rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina bayan kammala zaman kotun.
Lamarin dai ya biyo bayan sanarwar da Ministan Harkokin Cikin Gida ya yi kwanaki bayan furucin Dr. Kurfi, inda ya ce jami’an DSS sun kama wasu da ake zargin shugabannin ’yan bindiga ne da suka dawo daga aikin Hajji ta filin jirgin saman Umaru Musa Yar’Adua International Airport.