Wasu ƙwararrun likitoci sun bayyana cewa talauci na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da ƙaruwa samun sabbin masu kamuwa da cutar HIV a Najeriya.
A cewarsu, matsin tattalin arziki na sa mutane da dama, musamman matasa da mata masu ƙaramin ƙarfi, shiga halayen da ka iya jefa su cikin haɗarin kamuwa da cutar.
Likitocin sun ce yaƙi da cutar HIV ba zai ta’allaka ga samar da magunguna da gwaje-gwaje kaɗai ba, domin akwai buƙatar magance matsalolin tattalin arziki da ke ƙara jefa mutane cikin haɗari.
Sun kuma yi kira ga gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu su ƙara zuba jari a shirye-shiryen rage talauci, wayar da kan jama’a da kuma faɗaɗa damar samun ayyukan lafiya domin rage yawaitar sabbin masu kamuwa da cutar.
A cewarsu, haɗa matakan inganta tattalin arziki da wayar da kan jama’a zai taimaka wajen rage yaɗuwar cutar HIV tare da inganta rayuwar al’umma.