Fitaccen mawaƙin Afrobeats, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya kare matakin da ya ɗauka na sanya sunayen yara 39 da malamai bakwai da aka sace a jikin rigarsa yayin wani taron da ya shafi Gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026.
A wata hira da ya yi da shirin Focus on Africa na BBC, Davido ya ce manufarsa ita ce jawo hankalin duniya kan halin da waɗannan yara da malamai ke ciki, yana mai cewa har yanzu ba a san inda suke ba.
Mawaƙin ya bayyana cewa bai yi hakan domin bata sunan Najeriya ba, sai dai domin amfani da muryarsa wajen wayar da kan jama’a da ƙara matsa lamba a ci gaba da neman waɗanda aka sace.
Ya ƙara da cewa akwai masu ganin bai kamata a riƙa bayyana irin waɗannan matsaloli ba saboda kare martabar ƙasa, amma a cewarsa, babu wata martaba da za a kare idan ana ci gaba da sace yara ba tare da an gano makomarsu ba.
Davido ya yi kira da a ƙara mai da hankali kan kare rayuka da ceto waɗanda aka sace, yana mai jaddada cewa wannan ya fi muhimmanci fiye da damuwa da yadda duniya za ta kalli ƙasar.