Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiZulum ya biya bashin gata na Naira Biliyan 5.81 ga masu ritaya

Zulum ya biya bashin gata na Naira Biliyan 5.81 ga masu ritaya

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya miƙa cak na Naira biliyan 5.81 domin biyan bashin kuɗaɗen gata ga ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya da kuma iyalan ma’aikatan da suka rasu.

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya miƙa cak na Naira biliyan 5.81 domin biyan bashin kuɗaɗen gata ga ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya da kuma iyalan ma’aikatan da suka rasu.

An gudanar da bikin miƙa cak ɗin a Fadar Gwamnatin Jihar Borno da ke Maiduguri, tare da halartar shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago da na masu fansho.

Zulum ya bayyana cewa daga cikin kuɗin, kimanin Naira biliyan 2.99 za a biya iyalan dukkan ma’aikatan gwamnati da suka rasu da ake bin su bashi, yayin da Naira biliyan 2.82 za a biya ma’aikatan da suka yi ritaya har zuwa watan Disambar 2022, ciki har da ma’aikatan Hukumar Gidaje ta Jihar Borno.

Gwamnan ya ce matakin na cika alkawarin da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe, yana mai ƙara da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da biyan haƙƙoƙin ma’aikata da masu ritaya. Ya kuma yi alƙawarin duba matsalolin ma’aikatan ƙananan hukumomi tare da tattaunawa da shugabanninsu domin samo mafita mai ɗorewa.

Kwamishinan Kuɗi na jihar, Lawan Umar Dalorima, da shugabannin ƙungiyar ƙwadago sun yabawa Zulum kan matakin, suna cewa zai rage wa masu fansho da iyalan ma’aikatan da suka rasu wahalhalu tare da ƙara musu kwarin gwiwa kan jajircewar gwamnati wajen kula da jin daɗinsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments