Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroHarin ’yan bindiga a Sokoto ya yi ajalin Hakimi, ɗansa da wasu...

Harin ’yan bindiga a Sokoto ya yi ajalin Hakimi, ɗansa da wasu mazauna ƙauye

Wasu ’yan bindiga sun kai mummunan hari ƙauyukan Kulodo da Kwance da ke Ƙaramar Hukumar Bodinga a Jihar Sokoto, inda suka hallaka Hakimin Kulodo, Alhaji Abubakar Tudu, tare da ɗansa da wasu mazauna yankin biyar.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kutsa cikin ƙauyukan ne da sanyin safiyar Asabar, lokacin da jama’a ke gudanar da sallar asuba.

Sun zo ne a kan babura da dama, inda suka riƙa harbe-harbe ba tare da kakkautawa ba.

Bayan kisan gillar, maharan sun kwashe dabbobi masu yawa daga yankin.

Sai dai ba su yi nasarar yin garkuwa da kowa ba.

Harin dai ya haifar da firgici a yankin, inda mata da yara da dama suka tsere daga gidajensu saboda fargabar sake dawowar maharan.

Sai dai har yanzu jami’an tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba zuwa lokacin wallafa wannan rahoto.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments