Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Ibadan ta soke hukuncin da Babbar Kotun Jihar Oyo ta yanke a baya, wanda ya bai wa ɗalibai Musulmi damar sanya hijabi a makarantar International School da ke ƙarƙashin Jami’ar Ibadan.
Hukuncin ya fito ne a ranar Juma’a, inda alkalai uku suka saurari ƙarar, kuma biyu daga cikinsu suka amince da soke hukuncin da ƙaramar kotun ta yanke.
Kotun ta bayyana cewa hukuncin Kotun Koli da ya halatta sanya hijabi ya shafi makarantun gwamnati ne kaɗai, ba makarantu masu zaman kansu ko waɗanda ke da ƙa’idojinsu na gudanarwa ba.
A cewar kotun, International School Ibadan ba ta cikin rukunin makarantun gwamnati da hukuncin Kotun Koli ya shafa, don haka ba za a iya amfani da wannan hukunci a kanta ba.
Da wannan hukunci, kotun ta tabbatar da cewa makarantar na da ikon ci gaba da aiwatar da dokokinta kan tsarin shigar ɗalibai, ciki har da batun sanya hijabi.