Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan zargin kafa wata hukuma ko ta bogi a cikin gwamnatin tarayya.
Atiku ya ce lamarin ya wuce zarge-zargen ƙirƙirar takardu na bogi kawai, yana mai cewa ya haifar da tambayoyi masu yawa kan yadda ake tafiyar da harkokin gwamnati.
Ya ba Shugaba Tinubu wa’adin mako guda da ya ƙaddamar da sahihin bincike tare da bayyana sakamakon binciken ga jama’a domin tabbatar da gaskiya da ɗaukar matakan da suka dace.