Rundunar ’yan sandan Jihar Ondo ta ceto wata mata mai shekaru 61, Misis Modupe Oladele, bayan musayar wuta da masu garkuwa da mutane a garin Owo.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Abayomi Jimoh, ya ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar 23 ga Yuni, lokacin da wasu ’yan bindiga suka kutsa gidan matar, suka yi garkuwa da ita tare da sace motarta kirar Toyota Matrix.
Ya ce jami’an ’yan sanda sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 2:50 na dare, inda suka bi sawun maharan har zuwa wajen Ojana Phase 3. A nan ne aka yi musayar wuta mai zafi tsakanin jami’an tsaro da maharan.
Rundunar ta ce maharan sun tsere zuwa cikin daji bayan sun gaza ci gaba da fafatawa, inda suka bar matar da suka sace. An ceto Misis Oladele lafiya, tare da ƙwato motarta.
An kuma samu harsasai da aka harba, takalmi da fitila a wurin da aka yi artabun. Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike domin kamo maharan da suka tsere, yayin da Kwamishinan ’Yan Sanda, Felix Ohagwu, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin tare da buƙatar al’umma su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai.