Kotun Tarayya da ke Gombe ta fara sauraron karar da aka shigar tana kalubalantar sahihancin tsayawar Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Jihar Gombe.
Mai shigar da karar, Alhaji Abdulkadir Hamma Saleh, ya bukaci kotun da ta yi duba kan yadda aka tabbatar da Pantami a matsayin dan takarar jam’iyyar, yana mai neman hukuncin da zai fayyace sahihancin takararsa.
Ana sa ran kotun za ta ci gaba da sauraron shari’ar a zaman da za a yi nan gaba.