Sojojin Operation Hadin Kai sun cafke wani mutum da ake zargi da yi wa kungiyar ISWAP leken asiri tare da taimaka mata wajen shirya hare-hare kan sansanonin sojoji a Jihar Borno.
Rahotanni sun ce dakarun Bataliya ta 212 da ke sansanin horaswa na FOB Chabbol ne suka kama mutumin mai suna Muhammad Shuaibu bayan samun bayanan sirri da suka nuna ana shirin kai hare-hare kan wasu sansanonin sojoji.
An kama shi ne da safiyar ranar 26 ga Yuni yayin sintirin tsaro da ake yi a kusa da sansanin.
Binciken farko ya nuna cewa ana zargin mutumin da hannu wajen shirya kai hari kan Bataliya ta 199 ta Rundunar Soji (Sansanin Sauro) da kuma FOB Chabbol.
A yayin bincike, ana zargin Muhammad Shuaibu ya amsa cewa kungiyar ta shirya kai harin ko da kuwa an kama shi ko kuma ba a kama shi ba.
Hukumomin tsaro dai na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.