Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiAna zargin fadan daba ya yi sanadiyyar kashe mutane uku a Kano

Ana zargin fadan daba ya yi sanadiyyar kashe mutane uku a Kano

Wata mata ta rasa ranta yayin da rikicin fadan daba ya barke a Jihar Kano

Rahotanni na nuni da cewa ana zargin rikicin ’yan daba ya yi sanadin mutuwar mutane uku a Ƙofar Nasarawa da ke tsakiyar birnin Kano.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na rana, inda aka ce ’yan daban sun fito kan tituna suna fafatawa da junansu da makamai, abin da ya haifar da firgici tare da dagula harkokin yau da kullum a yankin.

Majiyoyinmu sun tabbatar da aukuwar lamarin, inda suka ce jami’an ’yan sandan sun isa wurin tare da tarwatsa masu rikicin.

Har ya zuwa yanzu dai ba a fitar da cikakken bayanin hukumance ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments