Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeƘasashen Tekun Fasha na meman tabbacin Amurka kan yarjejeniya da Iran

Ƙasashen Tekun Fasha na meman tabbacin Amurka kan yarjejeniya da Iran

Ƙasashen yankin Tekun Fasha sun buƙaci Amurka ta tabbatar musu cewa duk wata yarjejeniya da za a cimma da Iran a nan gaba za ta yi la’akari da batutuwan tsaronsu da kuma kare Mashigin Hormuz.

Ƙasashen yankin Tekun Fasha sun buƙaci Amurka ta tabbatar musu cewa duk wata yarjejeniya da za a cimma da Iran a nan gaba za ta yi la’akari da batutuwan tsaronsu da kuma kare Mashigin Hormuz.

Rahotanni sun nuna cewa a lokacin rikicin baya-bayan nan, yawancin hare-haren ramuwar gayya da Iran ta kai sun shafi ƙasashen yankin.

An ce Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ke ziyara a halin yanzu, ta fuskanci hare-hare da makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙi kusan 2,800.

Bayan ziyararsa a UAE, Rubio zai wuce Kuwait domin ganawa da Sarkin ƙasar. Ita ma Kuwait ta fuskanci hare-hare da suka shafi filin jirgin sama, tashoshin jiragen ruwa da cibiyoyin tace ruwan teku, waɗanda ke samar da kusan kashi 90 cikin 100 na ruwan sha na ƙasar.

Ƙasashen Tekun Fasha sun jaddada cewa suna son Amurka ta tabbatar da cewa duk wata yarjejeniya da za a cimma da Iran za ta kare tsaronsu da kuma tabbatar da zirga-zirga cikin aminci ta Mashigin Hormuz, wanda ke da matuƙar muhimmanci ga fitar da man fetur da iskar gas zuwa kasuwannin duniya.

SourceAljazeera
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments