Shugaban Amurka Donald Trump ya soki matakin da Majalisar Dattawan ƙasar ta ɗauka na amincewa da ƙudirin da ke neman a dakatar da duk wani matakin soja kan Iran ba tare da izinin Majalisar Dokoki ba.
Trump ya ce matakin sanatocin na aika saƙon rauni ga Iran, yana mai zargin cewa hakan na ƙarfafa abokan hamayyar Amurka.
Duk da amincewar majalisun biyu da ƙudirin, ana kallonsa a matsayin na alama ne kawai domin ba ya da cikakken ƙarfin doka.