An shiga jimami a sansanin tawagar ƙasar Faransa bayan rasuwar mahaifiyar babban kocin ƙungiyar, Didier Deschamps, a ranar Litinin.
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Faransa ta tabbatar da cewa Deschamps zai bar sansanin tawagar domin komawa ƙasarsa, inda zai kasance tare da iyalansa tare da yi wa mahaifiyarsa bankwana na ƙarshe.
Sakamakon wannan rashi, Deschamps ba zai kasance a bakin layin wasa ba lokacin da Faransa za ta kara da Norway a wasansu na ƙarshe na rukuni a gasar cin Kofin Duniya ta FIFA 2026.
Rahoton ya ce mataimakan kocin ne za su jagoranci tawagar Faransa a wasan, yayin da Deschamps ke halartar jana’izar mahaifiyarsa.
Rasuwar ta jawo saƙonnin ta’aziyya daga magoya bayan ƙwallon ƙafa, ‘yan wasa da masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na duniya, waɗanda suka miƙa addu’o’i ga Deschamps da iyalansa.