Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeAmurka ta dage takunkuman makamashin mai na Iran na wucin gadi

Amurka ta dage takunkuman makamashin mai na Iran na wucin gadi

Ma’aikatar Baitul Malin Amurka ta sanar da ɗage takunkuman da ta ƙaƙaba wa Iran kan fannin makamashin mai, inda ta bai wa ƙasar damar sake sayar da ɗanyen mai da sauran makamashi a kasuwannin duniya.

Ma’aikatar Baitul Malin Amurka ta sanar da ɗage takunkuman da ta ƙaƙaba wa Iran kan fannin makamashin mai, inda ta bai wa ƙasar damar sake sayar da ɗanyen mai da sauran makamashi a kasuwannin duniya.

Matakin zai fara aiki nan take kuma zai ci gaba har zuwa ranar 21 ga watan Agustan 2026, lokacin da ake sa ran kammala sabbin tattaunawa da ake yi tsakanin ɓangarorin biyu.

Sakataren ma’aikatar, Scott Bessent, ya bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne sakamakon ci gaban da aka samu a tattaunawar diflomasiyya, musamman dangane da batun buɗe mashigin Hormuz.

Haka kuma, Amurka ta ce Iran ta amince da dawowar jami’an Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya, IAEA domin sa ido kan ayyukan makamashinta.

Rahotanni sun nuna cewa an samu ci gaba a tattaunawar da ke gudana a Switzerland, bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a baya, wadda ta buɗe hanyar ci gaba da tattaunawa kan muhimman batutuwa tsakanin ƙasashen biyu.

SourceRFI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments