Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaRarara ya dora alhakin matsalolin Najeriya kan Kwankwaso

Rarara ya dora alhakin matsalolin Najeriya kan Kwankwaso

Rarara ya bukaci a bai wa kananan hukumomi cikakken ikon sarrafa kudaden su domin inganta ci gaban karkara.

Shahararren mawakin siyasa, Dauda Adamu Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara, ya dora alhakin wasu daga cikin matsalolin tattalin arziki da na mulki da Najeriya ke fuskanta kan tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Rarara ya bayyana hakan ne yayin wata hira da kafar yada labarai ta SL Update, wadda aka wallafa a TikTok ranar Lahadi, 21 ga Yunin 2026.

A cewarsa, matsalolin da kasar ke fama da su sun samo asali ne tun daga lokacin da aka fara rike kudaden kananan hukumomi a matakin jiha, maimakon a bai wa kananan hukumomi cikakken ikon tafiyar da kudaden su.

“Duk wahalar da Najeriya ke ciki yanzu ta samo asali ne daga lokacin da aka fara rike kudaden kananan hukumomi. Rike wadannan kudade tamkar rike jijiyar rayuwar al’umma ne,” in ji Rarara.

Ya kara da cewa rashin cin gashin kai na kudi ya kawo tsaiko ga ci gaban kananan hukumomi, musamman wajen aiwatar da ayyukan ilimi, kiwon lafiya, samar da ruwa da sauran muhimman ayyukan more rayuwa.

Mawakin ya jaddada cewa idan ana son ganin ci gaba mai dorewa a Najeriya, wajibi ne a bai wa kananan hukumomi cikakken ikon gudanar da harkokinsu da kudaden su ba tare da katsalandan daga wasu matakan gwamnati ba.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ko wakilansa ba su fitar da wata sanarwa ko martani kan wadannan kalamai ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments