Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiDan gwagwarmaya Sowore ya isa kotu bayan an bayar da umarnin kamo...

Dan gwagwarmaya Sowore ya isa kotu bayan an bayar da umarnin kamo shi

Omoyele Sowore, ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar AAC, ya isa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Litinin domin shari’arsa, bayan da kotu ta bayar da umarnin a kama shi.

Omoyele Sowore, ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar AAC, ya isa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Litinin domin shari’arsa, bayan da kotu ta bayar da umarnin a kama shi.

Sowore, wanda kuma shi ne mai wallafa jaridar Sahara Reporters, ya isa kotun tare da wasu mambobin ƙungiyarsa, inda suke rike da allunan zanga-zanga.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN ya ruwaito cewa Mai Shari’a Mohammed Umar ya soke belin da aka taɓa ba Sowore a ranar 16 ga Yuni, bayan ya gaza halartar zaman kotu na shari’arsa.

Mai shari’ar, a cikin hukuncinsa kan buƙatar da lauyan Hukumar Tsaro ta DSS, Akinkolu Kehinde, SAN, ya gabatar a baki, ya kuma bayar da umarnin kama Sowore.

DSS na tuhumar Sowore ne kan zargin yin kalamai na ƙarya game da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, inda ya kira shi “mai laifi” a sakonnin da ya wallafa a shafukan sa na X da Facebook.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments