Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta gabatar da wasu tsauraran sharudda ga ƙasar Benin kafin a sake buɗe iyakar da ke tsakanin ƙasashen biyu, wadda aka rufe tun bayan rikicin diflomasiyya da ya biyo bayan juyin mulkin Nijar na 2023.
Rahotanni sun nuna cewa wata babbar tawaga ta Nijar ce ta gabatar da buƙatun a lokacin tattaunawar da aka gudanar a ranar Lahadi, a matsayin mataki na samun daidaito tsakanin kasashen.
Manjo Janar Mohamed Toumba, wanda ke cikin manyan jami’an majalisar mulkin soji ta CNSP kuma ministan tsaron cikin gida, ya bayyana cewa batun sake buɗe iyakar zai dogara ne kacokan kan amincewar Benin da waɗannan sharudda.
Sharuddan sun haɗa da:
Na farko, kulla yarjejeniyar tsaro ta dindindin da za ta haramta kai farmaki ko amfani da ƙasar ɗaya wajen kai hari kan ɗaya, tare da tabbatar da zaman lafiya da rashin tsoma baki a harkokin juna.
Na biyu, samar da cikakken bayani kan dukkanin sojojin ƙetare da ake zargin suna kusa da iyakokin ƙasashen, tare da kafa tsarin haɗin gwiwar tattara bayanan sirri domin tunkarar matsalar tsaro da ta shafi yankin.
Wadannan matakai na zuwa ne a daidai lokacin da dangantakar Nijar da Benin ke ci gaba da fuskantar ƙalubale tun bayan sauyin mulki a Yamai a shekarar 2023.