Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin tsare ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, a gidan gyaran hali na Kuje.
Alƙalin kotun, Mai Shari’a Muhammad Umar, ya yanke hukuncin cewa Sowore zai ci gaba da zama a tsare har sai an saurari buƙatar da sababbin lauyoyinsa suka shigar, wadda ke neman a soke umarnin da ya soke belinsa da kuma sammacin kama shi.
A zaman da ya gabata, kotu ta soke belin Sowore bayan ya gaza halartar shari’a, yayin da masu gabatar da ƙara suka zarge shi da jan lokaci wajen tafiyar da shari’ar.
Har ila yau, kotun ta yi watsi da buƙatar Sowore na neman Mai Shari’ar ya janye daga sauraron shari’ar bisa zargin nuna son kai.