Saturday, October 17, 2026
HomeIlimiJAMB ta soke tsarin karatun digiri na haɗin gwiwa da kwalejojin ilimi

JAMB ta soke tsarin karatun digiri na haɗin gwiwa da kwalejojin ilimi

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Najeriya (JAMB) ta sanar da soke tsarin karatun digiri na haɗin gwiwa (Affiliation Programme) da ake gudanarwa tsakanin jami’o’i da kwalejojin ilimi (Colleges of Education) a faɗin ƙasar.

Hukumar ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan sauye-sauyen da aka samu a fannin ilimi, inda kwalejojin ilimi da dama suka samu damar ba da takardar digiri kai tsaye, maimakon dogaro da haɗin gwiwa da jami’o’i.

JAMB ta ce matakin zai taimaka wajen daidaita tsarin bayar da guraben karatu da kuma inganta gudanar da shirye-shiryen digiri a manyan makarantun ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments