Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAn naɗa CSP Anietie Iniedu a matsayin sabon Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan...

An naɗa CSP Anietie Iniedu a matsayin sabon Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya

Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya ya naɗa CSP Anietie Okokon Edem Iniedu a matsayin sabon Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta Kasa.

Kafin wannan naɗin, CSP Anietie Iniedu ya kasance Shugaban Sashen Karɓar Korafe-korafe a Hedikwatar Rundunar da ke Abuja, inda ya jagoranci ayyukan karɓar ƙorafe-ƙorafen jama’a tare da ƙoƙarin ƙarfafa gaskiya da amincewar al’umma ga rundunar.

Haka kuma, ya yi aiki a sassa daban-daban na rundunar ‘yan sanda, ciki har da jihohin Yobe da Abia, inda ya riƙe muƙamai daban-daban a fannonin gudanar da ayyukan tsaro da tabbatar da doka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments